in

Jami’o’i Amurka 2 sun janye digirin girmamawa da suka baiwa Donald Trump

Jami’o’in Lehigh University da Wagner College sun bayyana cewa zasu janye digirin girmamawa da suka baiwa shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump bisa yadda ya jawo wa kasar Amurka zubewar kimar ta a idon duniya saboda rikicin da ya faru a makon da ya gabata

Manuniya ta ruwaito Trump ya karbi digirin girmamawa a jami’ar Lehigh a shekarar 1988 bayan wani jawabi da ya gabatar sannan ita ma jami’ar Wagner ta girmama shi a shekarar 2004.

Sai dai duka jami’o’in sun ce dole zasu janye wadannan girmamawa saboda rashin darajar da Trump yayi bayan da magoya bayansa suka kutsa ginin majalisar Amurka wanda ya jawo mata dariya a kasashen duniya

APC ta yi Allah wadai da Amurka ta yi kira ga Donald Trump yayi koyi da Buhari

Gwamnati ta ce babu tabbas za’a koma makarantu a ranar 18 ga watan Janairu