Shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Amurka Joe Biden ba
Trump ya fadi haka ne a shafinsa na Twitter a yau Juma’a inda ya ce “duk masu tambayar za je bikin rantsar da Joe Biden ranar 20 ga watan Janairu ko a’a, to ku sani a’a ba zani ba”