Addini da RayuwaAlbum/EP

Bashir ya farka bayan dan jarida yayi masa tonon silili –tallafinsa yabi gida-gida

Hadimin shugaban kasa a fannin sadarwa, Bashir Ahmad ya kafa wata Gidauniya wacce ta fara bi gida-gida tana tallafawa marayu da gajiyayyu da mararsa lafiya a garin Kano da kewaye tana agaza masu da kudaden magani da abinci.

Manuniya ta ruwaito Gidauniyar mai suna “Bashir Ahmad Foundation” (BAF) ta dauki damarar taba zuciyoyin jama’a a ciki da wajen garin Kano “amma dai yanzu ta dukufa fara aiki ne daga mahaifar Bashir din dake Gaya a jihar Kano

Gidauniyar Bashir Ahmad a wani gida a garin Gaya

Cece-kuce da korafi akan Bashir

Kafin wannan lokaci dai ana yawan samun cece-kuce da guna-guni akan cewa hadimin shugaban kasar na sanyi-sanyi wajen yiwa jama’arsa hidima kamar yadda takwarorinsa na kudanci, irinsu Bayo da Tunde ake gani suke yiwa jama’ar yankinsu na tallafi

Bashir ya farka bayan wani gogaggen dan jarida yayi masa tonon silili

Ana iya cewa abubuwa sun sauya bayan da wani fitaccen dan jarida a jihar Kano mazaunin jihar Gombe, Abdulkadir Aliyu Shehu (Prince Abdulkadir Sardauna) ya yiwa hadimin shugaban kasar tonon silili inda ya zabi Bashir Ahmad a matsayin gwarzon shekara ta 2020, Sardauna ya fallasa wa duniya cewa akwai dumbin abubuwa da hadimin shugaban kasar ke yi amma baya fallasawa.

Prince ya ce Bashir Ahmad ya samar wa mutane da dama aiki, sannan yana yawan raba kayan tallafi a gidajen Talakawa da gajiyayyu, ko a lokacin kullen korona Mista Bashir ya yi ta bayar da tallafi, sannan yana baiwa jama’a jarin sana’a da kuma shige-da fice domin ganin an kawo aikin more rayuwa a yankinsu musamman mahaifarsa ta Gaya.

Tallafin Bashir Ahmad Foundation

“Wannan matashi yana yin hidimar zumunci sosai a tsakanin matasa kuma dayawa sun san a sanadiyyarsa sun samu aikin Gwamnati da sana’oi.” Sai dai ana iya cewa a yanzu da ya kafa Gidauniyar BAF zai rika fallasa abubuwan da yake yi domin jama’a su kara tabbatarwa musamman bayan da jama’a suka rika cece-kuce cewa “sallah da zumin dan siyasa ne kadai ya kamata ya boye amma dole ya bayyana ayyukan alkhairin da yake yi don karfafa wasu da kuma fita zargi duk da cewa don Allah yake yi amma dai jama’a su shaida”

Tallafin Korona na BAF

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button