Addini da RayuwaLabarai

Trump ya ce zai mika mulki bayan da majalisa ta tabbatar da nasarar Joe Biden

A karshe dai an bayyana Joe Biden da Kamala Harris a matsayin zababben shugaban kasar Amurka na 59 da mataimkiyarsa a hukumance.

Wannan ya faru ne bayan da gamayyar majalisar dokoki da Sanatocin kasar suka yi zaman tabbatar da nasarar tashi a ranar Laraba inda bayan tafka muhawara yan majalisa 282- suka amince da nasarar Joe Biden a yayinda 138 suka ki amincewa. Hakan tasa Joe Biden ya lashe kuri’un da mafi rinjaye.

Magoya bayan Donald Trump sun tayar da kura a farko har suka mamaye ginin majalisar suka fatattaki gamayyar yan majalisa da sanatocin har ma da mataimakin shugaban kasa Pence lamarin da yasa dole aka gaggauta kwashesu zuwa wata mabuya dake kasan ginin majalisar.

Bayan da gamayyar yan sanda da sojoji suka shawo kan rikicin tare da korar masu zanga-zangar daga ginin majalisar sai Sanatoci da yan majalisar suka sake komowa suka karasa zaman majalisar a tsakiyar daren ranar Laraba har zuwa wayewar garin ranar Alhamis.

Yadda masu zanga-zanga magoya bayan Trump suka haura ginin majalisar dokokin Amurka a daren ranar Laraba

Daga Bisani kamfanin Facebook da Twitter da YouTube suka sanar da dakatar da shafukan shugaba Donald Trump bisa yadda yake ta tunzura zanga-zangar ta hanyar sanya wani bidiyo da yayi ikirarin cewa shi yaci zabe ba Biden ba don haka ba zai yarda da sakamakon zaben ba.

Sai dai bayan da majalisar ta tabbatar da nasarar Joe Biden a matsayin sabon shugaban Amurka Donald Trump din ya fitar da wani sako inda a ciki yake cewa zai mika mulki duk da cewa yasan magudi akayi masa. A bisa ala’adar kasar Amurka dai a ranar 20 ga watan Janairu ne ake rantsar da sabon zababben shugaban kasa.

Hukumomi sun ce rikicin zanga-zangar ya jawo mutuwar akalla mutum daya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button