Labarai

Majalisa ta bukaci mataimakin Trump yayi masa juyin mulki ko kuma su tsige shi da kansu

Shugabar majalisar dokoki ta kasar Amurka Nancy Pelosi ta buƙaci mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya gaggauta yin amfani da sashin dokar kasar na “25th Amendment” ya tsige shugaban kasa mai barin gado Donald Trump.

Nancy a wani taron manema labarai da tayi ta ce abun kunyar da ya faru jiya a Amurka ya nuna lallai Trump mutum ne mai hadarin gaske, kuma kasar Amurka na cikin hadari muddin aka barshi har zuwa ranar 20 ga watan Janairu ranar da zai mika mulki ga Joe Biden

Saboda haka “ko dai Pence ya amshi mulki ko kuma su tsige Mista Trump kafin ranar rantsar da sabuwar Gwamnati”

Manuniya ta ruwaito Dokar sashi na “25 Amendments” dai ta bayar da dama ga Mataimakin shugaban kasa da majalisar zartarwar kasar suna iya zama su tsige shugaban kasa mai ci muddin aka same shi da wata gazawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button