Addini da RayuwaAlbum/EPLabaraiWasanni

Magidanci dan shekara 45 ya yiwa diyarsa yar shekara 13 fyade a Ogun

Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani magidanci dan shekara 45, mai suna Akanji Oluwaseyi, a bisa zarginsa da yi wa diyarsa yar shekara 13 fyade.

Manuniya ta ruwaito diyar Mista Akanji mazaunin garin Obantoko dake Abeokuta a jihar Ogun ta shaidawa rundunar yan sanda cewa mahaifin nata ya kirawo ta daga shagon da take koyon dinki ya aike ta ta dibo mashi ruwa inda bayan ta dibo ruwan ne ta shiga gida sai ya bi ta ya danne har ya yi mata fyade.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 30 ga watan Disamba da ta gabata.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce da farko mahaifin yarinyar ya musanta faruwar lamarin amma bayan da aka kai yarinyar asibiti sannan kuma ta maimata labarin abunda ya yayi mata a gabansa sai ya kidime ya dimauce.

DSP Abimbola ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Edward Ajogun ya tura batun zuwa sashin binciken manyan laifuka

Mahaifin yarinyar Mista Akanji Oluwaseyi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button