Innalillahi wa’inna ilaihir-raji’un Korona ta kashe kanin mataimakin Gwamnan jihar Lagos, Dr. Obafemi Hamzat mai suna Haroun.
Haroun Hamzat kwararren matashin likita ne dake aiki a daya daga cikin asibitocin kiwon lafiya na Gwamnati dake Orile Agege LCDA.
Manuniya ta ruwaito margayin ya rasu ne a jiya Talata yana da shekara 37 a duniya.
Hukumar dakile yaduwar cutar korona, NCDC ta ce a jiya Talata kadai mutum 1,354 suka kamu da cutar ta Korona a Nigeria.

Ga jadawalinsu kamar haka:-
Lagos-712,
Abuja FCT-145
Plateau-117
Kwara-81
Kaduna-54
Sokoto-39
Oyo-38
Rivers-37
Gombe-21
Enugu-20
Akwa Ibom-16
Bauchi-14
Delta-14
Ebonyi-13
Anambra-9
Taraba-8
Edo-8
Kano-3
Osun-2
Ekiti-2
Ogun-1

Adadin masu Korona a jiya Talata ya kai 92,705
An sallami mutum 76,396
Sannan ciwon ya kashe mutum 1,319

