Labarai

Gwamnatin tarayya zata rika karbar rancen duk kudin da aka ajiye a banki aka rasa mai shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokokin harkalla da kudade na 2020 inda a ciki akwai bayanin wata doka da ta baiwa Gwamnati tarayya dama ta karbe duk wani kudi dake cikin asusun banki wanda aka rasa gane masu shi.

Dokar dai tayi tanadin cewa za a rika mayar da duk wani kudi a asusun banki wanda har ya kai shekara 6 ba a gane masu shi ba ko kuma ba ayi amfani dasu ba. “Amma dai za a tura a asusun Gwamnatin tarayya ne a matsayin rance”

Duk lokacinda mai kudin ko masu kudin ko kadarorin suka bayyana zasu iya yin magana a mayar masu da kudadensu ko dukiyarsu da Gwamnatin ta wawashe daga asusun bankunansu tunda dama rance ne

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button