Addini da RayuwaAlbum/EPLabarai

Wata Baturiya ta fadawa yan Afrika gaskiya game da allurar rigakafin Korona (karanta kuji)

Wata Ba-Amurkiya mai suna Tracy Zille ta yiwa Afrikawa wankin babban bargo inda ta fadi gaskiya mai daci akan yankin na Afrika ko kuwa muce Nigeria. Ga alamu dai Baturiyar ta fusata ne saboda cece-kucen da yan Afrika ke yi game da rigakafin cutar korona da turawa sukayi amma bakin fata ke korafin cewa akwai lauje cikin nadi.

Zille a shafukan ta na sadarwa ta rubuta “Da ba dan mu ba da yanzu bakin ku na doyi kamar mataccen bera domin har yau baku iya yin ko man goge baki na kanku ba. Don haka ku rufe mana baki ku karbi allurar rigakafi ko kuma kuyita mutuwa.

Baturiyar ta lissafo duka man goge bakin da yan Nigeria talakawa da masu kudinsu ke amfani dashi sannan ta fadi kasar da ake yin shi

Ta ce “Man goge baki na Colgate (a Amurka ake hadashi), man goge baki na Aquafresh (A Britaniya ake hada shi), na Close Up (A Ingila ake hada shi), na Mentadent (A kasar Canada ake yin shi), na Oral-B (Amurka ke yin shi), Sensodyne kuma (a kasar Japan ake yin shi).

Amma Hamshakan Fastoci da Limami kuma (A Afrika ake yin su).

Muna yin man goge baki kuna yin addu’oi da ruwan rubutu, ko ace man addu’a (anointing oil da fastoci ke bayarwa a coci) domin neman sa’a ko rashin lafiya.

“Kada wanda ya zage ni dan na fadi maku gaskiya. Mu muna amfani da kudaden mu muna gina jami’oi da cibiyoyin bincike da kayan aikin kimiyya da fasaha ku kuma kuna amfani da kudaden ku wajen gina manya-manyan kayatattun coci da masallatai kuna sayawa fastocin ku da malaman ku manya-manyan motoci da gidaje na alfarma suna fantamawa.

Cibiyoyin binciken mu sun kirkiro rigakafin Korana cocinan ku sun kirkiro ruwan addu’a (anointing oil), kuna sanya manyan kudade kuna sayen ruwan addu’a a wajen fastocin naku ba tare da korafi ba amma kun zo kuna wani soki burutsu da surutai akan allurar rigakafin Korona da masana suka kirkiro aka ce za a yi maku a kyauta. Akwai alamun tabun hankali a tattare daku gaskiya… inji Baturiya Zille

Sakon da Tracy Zille ta rubuta a twitta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button