Addini da RayuwaAlbum/EPLabarai

Wani matashi a Bauchi ya kashe yaro ya cire idanunsa don yin kudi

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi Musa Hamza, dan shekara 22, bisa zarginsa da kashe wani yaro Adamu Ibrahim sannan ya cire masa idanuwa sai ya kona gawarsa ya bizne a Unguwar Wake dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi.

Manuniya ta ruwaito kakaki yan sandan Bauchi, DSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya amsa laifinsa kuma lamarin ya faru ne a ranar 21/12/2020.

Ya ce wanda ake zargin bayan ya kashe yaron ya kona gawar sai kuma ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa sannan ya bizne kowane sashin jikin a waje daban-daban.

Matashin ya amsa laifinsa kuma ya ce bokan sa ne ya saka shi aikata wannan ta’addaci domin yana so yayi kudi

Musa da kokon kan wanda ya kashe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button