in

KORONA: Gwamna Fintiri ya sa dokar kulle a Adamawa, ya haramta tarurruka

Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce a sakamakon rashin bin dokoki da ka’idojin kariya daga cutar korona a jihar Adamawa da mutane ke yi na wanke hannuwa, sanya takunkumin fuska, bayar da tazara daga yanzu ya haramta yin taro a fadin jihar

Mista Fintiri ya ce ya rufe duka cibiyoyin shakatawa, kulub-kulub, da tarurruka.

Kazalika ya bukaci malaman Addini su tashi tsaye wajen ganin mabiyansu sun bi dokikin kariya daga cutar a wuraren ibada.

Manuniya ta ruwaito Gwamna Fintiri na cewa dokar da ya sanya a watan Maris din 2020 tana nan daram saboda haka ya baiwa jami’an tsaro dama su tabbatar ana bin dokar.

“Sannan an haramta zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safiya daga nan har sai yadda hali yayi.

Amarya ta rasa budurcin ta wajen neman kudin yin “event” din auren ta

Magidanci dan shekara 45 ya yiwa diyarsa yar shekara 13 fyade a Ogun