Album/EPLabarai

Pantami ya raba lambobin wayar da za’a kai karar duk ma’aikacin da ya nemi a bashi kudi a wajen yin NIN

Ministan Sadarwa Dakta Isah Pantami ya bayar da umurnin  a dakatar da duk ma’aikaci daga aikinsa da aka samu yana karbar kudin jama’a kafin yi masu lambar zama dan kasa wato NIN.

Pantami ya sake jaddada cewa yin NIN kyauta ne a ko’ina kuma ba zasu lamunci wasu bata gari suna amfani da damar suna tatsar kudade wajen mutane ba.

Manuniya ta ruwaito akwai korafe-korafen karbar kudi a hannun jama’a da wasu ma’aikatan hukumar yin NIN din ke yi musamman a jihohin Kaduna da Bauchi

Sai dai Ministan sadarwar ya roki jama’a da su nada su aika da duk wata shaidar hoto, murya, ko bidiyo na duk wani ma’aikacin da ya nemi su bashi kudi su tura korafin zuwa lambobin waya kamar haka 08157691214; 08157691071 ko ta adreshin su na e-mail actu@nimc.gov.ng.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button