Labarai

Jarumin Dan sanda da yaki karbar cin hancin miliyan N864 ya ajiye aikin dan-sanda

Jami’in dan sandan Nigeria da ya taba kin karbar cin hancin Naira miliyan N864 ya yi murabus daga aikin dan sanda saboda sau Uku ana hana shi karin girma duk da ya cancanta.

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito jami’in Dan sandan mai suna Francis Erhabor, wanda ke jagorantar wani sashi na rundunar yan sanda a jihar Akwa Ibom, ya ce sau Uku duk da lokacin karin matsayinsa ya zo sai a cireshi, kuma ya kai kara anyi bincike an gano yana da gaskiya amma kuma babu wani mataki da aka dauka.

A watan Disamba 2020 ne dai tashar Igbere TV ta karrama Mista Erhabor a matsayin zakaran dan sandan 2020

To sai dai Kwamishinan yan sanda na jihar Akwa Ibom CP Amienghene Andrew ya ce bashi da labarin murabus din Mista Erhabor kamar yadda kakakin yan sandan jihar, Odiko MacDon ya fada a wata sanarwa

Ya ce Erhabor bai gabatar da yin marabus din shi a rubuce ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button