Labarai

Gwamnan Kwara ya sauke duka kwamishinoni da masu rike da mukaman Gwamnati da ya nada

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sauke duka Kwamishi, da masu rike da mukaman Gwamnati a jihar.

Manuniya ta ruwaito sanarwar ta ce Sakataren Gwamnatin jihar Kwara Farfesa Mamman Jubril ne kadai  saukewar bata shafa ba. “Mai girma Gwamna ya gode masu baki daya sannan ya bukaci kowannen su ya mikawa babban jami’i a ma’aikatarsa”

Kwamishinon dai duk an rantsar dasu ne a ranar 14 ga watan Disamba, 2019, a lokacin dai Gwamnan ya sha yabo ganin cewa mata ne suka fi rinjaye a rabon mukaman inda suke da akalla kaso 56.25%

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button