in

Buhariyya ta taba Atiku, ya sayar da babban kamfaninsa na “INTELS”

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sayar da babban kamfaninsa na Integrated Logistics Services Nigeria Limited, wato Intels.

Tun da farko dai kamfanin Intels din ne ya fitar da sanarwar cewa sun sallami Atiku da iyalansa daga kamfanin.

Hakan ya sa yan Nigeria sun shiga mamaki har sai a yammacin ranar Litinin da Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya tabbatar da labarin, inda yace tun wajen shekara 5 da ta gabata ya fara sayar da hannayen jarinsa dake kamfanin saboda ya ga wannan Gwamnatin na neman karyashi saboda rikicin siyasa.

Atiku da yayansa sun janye gabaki daya daga kamfanin.

Jarumin Dan sanda da yaki karbar cin hancin miliyan N864 ya ajiye aikin dan-sanda

Hajiya Asiya Balaraba Ganduje ce Gwarzuwata ta 2020 a cikin mata –El-Bash