Labarai

Tinubu ya ce karya ne bai kamu da korona ba kuma “sau 15 yana gwaji”

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu, ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa wai ya kamu da cutar korona har ma an kwantar dashi a kasar Faransa.

A wata sanarwa da kakakin Mista Tinubu ya fitar da yammacin yau Lahadi ya ce sau 15 tsohon Gwamnan Lagos din wato Mista Bola Ahmed Tinubu yayi gwajin cutar korona amma sakamakon gwajin ya nuna lafiyarsa kalau.

A cewar sanarwar Tinubu ya bar Nigeria ne domin yin hutun karshen shekara kamar yadda ya saba yi a duk shekara

Yan Nigeria dai na ta muhawara akan wannan lamari ganin cewa Tinubu yayi batan dabo daga Nigeria tun kafin karshen shekarar 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button