Labarai

Tambuwal ya nada Malam Abubakar a matsayin shugaban ma’aikatan jihar Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sokoto) ya nada Malam Abubakar Muhammad a matsayin shugaban ma’aikatan Gwamnatin jihar Sokoto

Manuniya ta ruwaito nadin nashi na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Sokoto, Alhaji Sani Garba Shuni ya yi ritaya bayan cikar wa’adinsa na aiki.

Daya daga cikin mataimakan Gwamnan Bilyaminu Yarima ya ce sabon shugaban ma’aikatan wanda ya kammala karatun sa na digiri, a Jami’ar Usman Danfodio, an haife shi ne a 4th January, 1967

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button