Addini da RayuwaLabarai

Ana zargin shugaban Bankin FCMB da yin lalata da matar aure har suna haihuwa

Daruruwan mutane sun sanya hannu kan wata takardar koke zuwa ga Babban Bankin Nigeria CBN suna neman a kori shugaban Bankin FCMB, Mista Adam Nuru bisa zarginsa da yin lalata da wata matar aure har mijinta ya mutu saboda kishi.

Manuniya ta ruwaito ana zargi mijin matar mai suna Mista Tunde Thomas ya hadiyi zuciya ya mutu ne sakamakon shiga ukun da yayi bayan da ya gano abunda ke wakana tsakanin matarsa Misis Moyo Thomas da Ogan nata manajan Bankin FCMB da take aiki.

Bayanai sun ce Misis Thomas ta shaidawa mijinta cewa za tayi wata tafiya daga Nigeria 0zuwa kasar Amurka tare da duka yaransu, sai dai bayan ta sauka Amurka ne sai ta kira mijin nata a waya take shaida masa cewa yayi hakuri fa domin duka ‘yayansu ba shine ubansu ba.

Tun daga nan mijin nata ya fada damuwa har ta kai ga ya rasa ransa.

Ana dai zargin ya’yan duka na ogan nata ne Shugaban bankin FCMB.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button