Labarai

Zulum ya roki Gwamnati ta kai wa yan gudun hijira a jiharsa kayan abinci

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya ziyarci hedikwatar hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, inda ya nemi hukumar da ta tallafawa yan gudun hijira dake jiharsa da suke fama da rashin abinci su fiye da dubu 800.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya ce akwai garuruwa 11, Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da Gajiram dake bukatar agajin gaggawa na kayan abinci.

Zulum ya kuma kai ziyara ga ministar harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyema a Abuja, inda ya roki ministar ta agaza a maido da yan jihar Borno dake gudu hijira a sansanin Minawawo dake kasar Kamaru su akalla dubu 60.

Zulum ya ce mutanen sun gudu kusan shekara 6 da ta wuce a sakamakon hare-haren ta’addanci a jihar Borno amma yanzu suna son dawowa gida Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button