Addini da RayuwaLabarai
El-Rufa’i ya rusa gidan da aka so yin casu maza da mata tsirara (kalli hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayar da umurni a rushe Asher Hotel wani gidan casu da aka shirya yin bikin nuna tsiraici a cikinsa a makon da ya gabata.
Idan dai baku manta ba Manuniya ta kawo maku rahoton yadda Gwamnan ya dakatar da gudanar da wani casun dare da aka shirya a jihar Kaduna inda maza da mata zasu halarta tsirara sannan aka tanadi mata 50 da suka amince ayi zinace-zinace dasu.
A wancen lokacin Gwamnatin Kaduna baya ga hana casun badalar ta kuma kama wadanda suka shirya taron.
Kalli hotonun rusa gidan casun na Asher Hotel dake Barnawa Kaduna






