KannywoodLabarai

Mungode da addu’oi amma lafiya ta kalau Alhamdulillah –inji Sheikh Giro Argungu

Shehin Malamin addinin Musulunci dake jihar Sokoto Sheikh Abubakar Giro Argungu ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa bashi da lafiya wai ma har an kwantar dashi ko kuma an kai shi asibiti ranga-ranga (Emergency). Shehin malamin ya ce ya gode da jerin addu’oi amma Alhamdulillah lafiyarshi kalau.

A tattaunawar da Manuniya tayi da iyalan Shehin Malamin a yau Litinin sun ce “Mun samu labarin wasu suna yada cewa wai malam ba lafiya, to gaskiya dai yanzu haka gamu tare da malam yana zaune cikin amincin Allah”

Manuniya ta ruwaito Malamin ya yi fama da zazzabin Maleria kwana 2 kuma tun daga nan ya samu sauki cikin ikon Allah.

“Ganin cewa ba a samu yin karatu jiya da shekaran jiya ba shine yasa almajiran malam da sauran mutane suka yi zaton ko rashin lafiyar ce amma ba haka din bane gaskiya.”

Da Manuniya ta tambayi ko malam zai fito ko da a bidiyo ne ya yi bayani domin hankulan jama’a su kwanta “To kasan irin wadannan jita-jita suna nan da yawa ana yada su idan muka ce komi sai mun maida martani abun ba zai bayar da wata fa’ida ba amma dai muna nan muna bin al’amarin idan mun ga da bukatar mu karyata to malam zai yi bidiyo ko wani abu makamancin wannan domin karyatawa da kwanatar da hankulan jama’a”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button