Addini da RayuwaAlbum/EPLabarai

Gwamnati ta hana wani casu da aka so yi tsirara a Kaduna –ta kama wadanda suka shirya shi

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da samun nasarar hana gundanar da wani casu dare na badala da aka shiryawa matasa maza da mata zasu bayyana tsirara suyi rawa su, su ci abinci su yi shaye-shaye sannan kuma ayi zinace-zinace domin murnar shiga sabuwar shekara

A katin gayyatar zuwa casun an saka sharadin dole ne mutum ya je tsirara, sannan da kororon roba, kanan kuma aka saka kudin shiga daga Naira 2,000, da VIP 5,000 da kuma VVIP 10,000

Sun rubuta a jikin katin cewa sai mutum ya biya kudinsa sannan za a bayyana masa wajen da za ayi casun amma dai masu shirya taron sun bayyana cewa akwai zafafan mata 50 da zasu nishadantar da mahalarta taron sannan dukansu mutum na iya saduwa dasu a lokacin casun

Sai dai shugaban kula da harkokin addinai na jihar Kaduna Sheikh Albani a safiyar yau Litinin ya ce “Cikin Ikon Allah munsamu Ikon hana wannan rashin mutuncin da kama Wanda suka shirya. Mai girma Gwamna Mallam Nasiru El-Rufa’i muna GODIYA.”

Hakanan shima mai taimakawa Gwamnan Kaduna a fannin yada labarai Abdallah Yunus Abdallah ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Mun godewa Gwamnati bisa hobbasan da tayi wajen ganin ta hana wannan badala”

Gwamnatin dai ta ce bayan hana casun da tayi sannan kuma ta kama wadanda suka shirya shi domin hukunta su.

Katin gayyatar zuwa casun

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button