Addini da RayuwaLabarai

Gwamnatin Kaduna ta rufe wasu otel da mashaya da suka karya dokar kulle

A kokarin ganin ana bin doka da oda dangane da dakile yaduwar cutar korona a jihar Kaduna, Gwamnatin jihar a karkashin ma’aikatar kula da kasuwanci ta rufe wasu otel-otel da mashaya da wuraren abinci da kasuwanci wadanda suka karya doka.

Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe  Lesham Luxury Hotel, dake Barnawa sakamakon kin rufe mashayar otel din da kuma kududdufi  wanka dake otel din.

Sannan an rufe otel din Standard Hotel, Majalisa, dake Television shima sun ki rufe mashayar su.

Gwamnatin ta kuma rufe mashayar Monti Bar, dake Peugeot Junction sakamakon sun bude mashayarsu.

Gwamnatin dai na bi lungu da sakon jihar domin tabbatar da ana bin doka da oda a fadin jihar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button