Addini da RayuwaAlbum/EPHausa Songs

JI KA KARU: Karas na dauke da wasu surrika ga lafiyar jiki ga guda 7 daga ciki

JI KA KARU: Tare da Aisha Aliyu Shanono


Mutane da yawa na amfani da Karas wasu na ci danye wasu kuma suna amfani da shi wajen kawata girki amma akasarin mutane basu san amfanin shi a jikin dan Adam ba.


Karas na dauke da sinadarai da dama domin yana taimakawa wajan kara lafiya da kuma kare mutane daga wasu cututuka kamar haka.

1. Ciwon ido: Karas na dauke da sinadarin vitamin “A” wanda yake karfafama idanu wajan gani.

2. Gyaran fata: Karas na dauke da sinadarin ‘carotenoids’ wato sinadarin dake haskaka fata ya sanya ta tayi kyau

3. Ciwon daji: Karas na dauke da sinadarai masu dumbin yawa, wanda ya hada da “phytochemical” da ke yaki da cututukan daji, yana kuma karfafa garkuwan jiki da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji

4. Kwarin Kashi: Sinadarin da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin halita daga cututuka yana kuma inganta lafiyar ‘kashi

Ana iya sarrafa karas yadda ake so5. Rage kitse: Idan mutum yana bukatan rage kitsan dake jikin shi to ya luzumci cin danyen karas domin yana dauke da sinadarin “lectin” mai taimakawa wajen rage kitse.

6. Ciwon Baki da hakora: Cin danyan Karas na taimakawa wajan magance cututukan baki da hakori kuma yana bada numfashi mai inganci

7. Ciwon hanta: Karas na dauke da “beta carotene” da “vitamin A” wanda suke inganta lafiyar hanta da ba ta kariya daga kamuwa daga wasu cututtukan.

Karas na da amfani da dama ga lafiyar jiki


Karas na taka muhinmiyar rawa a jikin dan adam kuma dama yanzu lokacin shi ne da fatan za a lazumci
cin karas, mai gida da uwar gida …rugakafi dai aka ce ta fi magani. Ku biyo mu a shiri na gaba a cikin filin JI KA KARU tare da ni yar’uwar ku Aisha Aliyu Shannon domin jin wani sabon maudu’in!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button