Labarai

Gwamna Lalong na jihar Plateau ya warke daga cutar korana

Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya warke daga cutar korona da ya kamu da ita a makon da ya gabata kuma tuni ya dauki haramar komawa ofishinsa domin cigaba da aiki.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan a ranar 17 ga watan Disamba ya mika mulkin jihar kana ya killace kansa saboda gwaji ya nuna ya kamu da korona.

Gwamnatin jihar Plateau ta fitar da sanarwar cewa likitoci sun sake yi masa jerin gwaje-gwaje kuma a daren jiya Laraba sun tabbatar masa ya warke kuma yana iya cigaba da harkokin sa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button