Album/EPLabaraiWasanni

Hadarin mota ya kashe Fasinjoji 12, ya raunata 25 a hanyar Kaduna-Abuja

Akalla fasinjoji 12 sun mutu kana kuma wasu 25 sun ji raunuka a sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya rutsa dasu yau Laraba a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Tuni dai Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya tura tawaga zuwa wajen da abun ya faru inda aka kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.

Kazalika hadarin ya jawo mutuwar dumbin dabbobi.

Manuniya ta ruwaito hadarin ya faru ne bayan wani mai mota a guje da ya biyo “one way” ya gittawa wani mai trela da ya dauko kaya wanda nan take trelar ta kwace masa inda ta tuntsura akan titi lamarin da ya jawo mutuwar fasinjojin dake motocin dake biye da trelar

Elrufai ya jajantawa iyalan mamatan da mararsa lafiyar kana kuma ya shawarci masu ababen hawa su guji mugun-gudu da kuma dibar kayan da ya fi karfin motocinsu, sannan ya jaddada cewa dokar da ya saka ta “haramtawa masu ababen hawa bin one way na nan daram kuma zasu dauki mataki kan masu karyawa”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button