in

DA DUMI-DUMI: Bayan kwashe wata 9, ASUU ta janye yajin aiki

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nigeria ASUU a yau Laraba ta sanar janye yajin aikin da take yi sakamakon cimma yarjejeniya da tayi da Gwamnatin tarayya.

ASUU dai ta fara yajin aikin ne tun a watan Maris din shekarar 2020 wato akalla wata 9 kenan.

Shugaban ASUU na kasa Biodun Ogunyemi ne ya bayyana sanarwar da safiyar yau a Abuja.

ASUU ta bayyana cewa ta amince da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata ne shi ya sa ta amince da janyewa bayan tsawon wata tara amma kuma zata iya komawa yajin aiki ba tare da wani gargadi ba muddin Gwamnatin ta taka yarjejeniyar.

Buhari ya umurci ma’aikatan Gwamnati mataki na “12” su daina zuwa Ofis, su rika aiki daga gida

Hadarin mota ya kashe Fasinjoji 12, ya raunata 25 a hanyar Kaduna-Abuja