Labarai

Zulum yaji zafin sace fasinjoji 30 -zai gana da kwararru kan tsaron hanyar Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce abun takaici ne yadda ake cigaba da samun yawaitar hare-hare da satar fasinjoji a babbar hanhar Maiduguri zuwa Damaturu musamman ma a daidai kauyen Jakana inda harin yafi yawaita.

Zulum ya ce da kanshi ya taso daga gidan Gwamnati har zuwa garin Jakana inda aka sace matafiya akalla 30 a makon da ya gabata amma abun bakin ciki da takaici ko Soja daya bai gani a hanya ba balle JTF duk kuwa da irin dumbin gudummuwar da suke samu daga Gwamnatin tarayya da Gwamnatin jihar Borno amma sun kasa daukar matakin tsaro a kan hanyar wacce bata wuce kilomita 20 ba.

Ya ce “idan kun kasa bayar da tsaro a hanyar da bata wuce kilomita 20 ba daga Auno zuwa Jakana to ta yaya kuke so mu yarda cewa zaku iya gamawa da Boko Haram”

A cewar Gwamnan  “Mafi yawan hare-haren ta’addanci da satar mutane a hanyar Maiduguri-  Damaturu-  Kano sun fi faruwa ne a tsakanin Auno zuwa Jakana.”

Saboda haka Gwamnan ya sha alwashin zai gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki akan tsaro domin lalubo mafita da kare matafiya a wannan hanya mai muhimmanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button