Labarai

Yan Nigeria su godewa Allah da zuwan Buhari Bama-Bamai sun daina tashi kullum -inji Fadar Shugaban

Fadar shugaban kasa ta shawarci yan Nigeria su rika godewa Allah suna yabawa dan sassaucin da suka samu dangane da tsaro a karkashin mulkin shugaban kasa Manjo-Janaral Muhammadu Buhari.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce kafin zuwan Gwamnatin Buhari a da kullum sai bama-bamai sun tashi a Nigeria kamar ana harba banga amma yanzu shiru kaka ji. Yace wannan abun a godewa Allah ne sannan a yabawa Buhari bisa kokarin da yake yi ta fuskar samar da tsaro a kasarnan.

Manuniya ta ruwaito Adesina ya cigaba da zayyana cewa matsalar tsaro abu ne da ya addabi kasashen duniya domin a yanzu har manyan kasashen duniya da suka cigaba suna fama da matsalar tsaro.

Sai dai Adesina na magana ne a daidai lokacinda ake fargaban kamar yan ta’adda na dada samun karfi a Nigeria musamman ganin yadda garkuwa da mutane da kashe-kashen rayuka ke neman zama ruwan dare a kasar.

Domin ko a makon da ya gabata sai da aka sace yara dalibai akalla 344 da kuma wasu daliban su akalla 80 kodayake dai duka an ceto daliban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button