Labarai

Sarki a Zamfara na roko Gwamnati ta yarda kowa ya mallaki makami domin kare kansaShugaban Sarakunan jihar Zamfara, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, ya roki Gwamnantin jihar ta amince jama’a su rika mallakar makamai domin kowa ya rika kare kansa daga hare-haren yan ta’adda da ya yi kamari a jihar.

Attahiru, ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya gun Sarkin Kaura-Namoda wanda yan bindiga suka kaiwa tawagarsa hari a makon da ya gabata har suka kashe masa mutum 8,


Sarkin ya ce “tunda yan ta’addan basa son zaman lafiya kuma basa tsoron Gwamnati to a bari kawai kowa ya rike makami ya kare kansa domin babu gagararre sai bararre”

A cewar basaraken shirin sulhu da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kirkiro ba zai kawo karshen hare-haren ba domin yan ta’addan ba zasu taba mika wuya a samu zaman lafiya ba.

“Babu mahalukin da ya fi karfin Gwamnati sai dai idan Gwamnatin ce bata so daukar mataki ba.” inji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button