Labarai

Nigeria ta rasa kujera a Kotun Duniya bayan dan takarar Buhari ya sha kasa

Dan takarar da shugaban kasa Manjo-Janaral Muhammadu Buhari ya tura domin ya wakilci Nigeria a kotun daukaka kara ta duniya, Ishaq Bello ya sha kasa a zaben da kotun tayi, saboda haka Nigeria ta rasa kujerar a bana.

Bello dai shine Shugaba Alkalan Babban kotun tarayya ta Abuja wanda shugaban kasa Buhari ya zabe shi daga cikin alkalai 20 yan Nigeria ya tura sunansa domin ya fafata a zaben zama lauya a kotun duniyar wato ICC.

Manuniya ta ruwaito daga hedikwatar, ICC, dake birnin Hague a kasar Netherlands cewa a karon farko Bello ya samu kuri’u 12 daga cikin kuri’u 117.

A zagaye na biyu kuma sai ya samu kuri’u 5 daga cikin kuri’u 110 da aka kada wanda hakan tasa ya rasa kujerar

Dama dai anyi ta korafin cewa akwai wadanda suka fi Bello cancanta daga cikin mutum 20 da aka gabatarwa da Buhari amma ya hakikance akan dan takarar nasa inda ya tura shi ya wakilci Nigeria a zaben wanda ya kunshi fiye da kasashe 18.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button