Labarai

Yan bindiga sun kai wa tawagar Sarkin Kauran Namoda hari sun kashe mutum 8

Yan bindiga sun kai hari kan tawagar Sarkin Kauran Namoda na jihar Zamfara Sanusi Muhammad, inda suka kashe akalla mutum 8.

Manuniya ta ruwaito daga majiyoyi cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis lokacinda sarkin ke dawowa daga Abuja.

Rahotanni sun ce yan bindigar sun kashe yan sandan 3 kana sun kashe wasu mutum 5 daga cikin tawagar sarkin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button