Album/EPLabarai

Satar daliban Kankara 344 da ceto su duk wasan kwaikwayo ne –inji Afenifere

Kungiyar kabilar Yarabawa, Afenifere, ta ce lokaci yayi da yan Nigeria zasu fargaba su farka daga bacci daga irin damfara da wasan kwaikwayon da yan siyasar kasar nan ke yi na wasa da kwa-kwalan jama’a domin cimma wasu buruka nasu.

A sanarwar da kungiyar ta fitar ta hannun kakakin ta, Yinka Odumakin ya ce zancen sace yara dalibai yan makarantar GSS Kankara da aka ce yan Boko Haram sunyi da kuma batun kubutar dasu da aka ce jami’an tsaro sunyi duk wasan kwaikwayo ne

A cewarsa akwai jerin tambayoyi da duk mai hankali zai zauna yayi game da faruwar lamarin wanda daga karshe zai gane cewa abun duk bige ce.

Sanarwar ta kara da cewa abun mamaki ne a ce tun daga jihar Katsina an kwashi daliban har su 344 an wuce duk shingen jami’an dake hanya har aka kaisu dajin jihar Zamfara.

Sannan abun da mamaki a ce fadar Shugaban kasa, ta bakin Garba Shehu ya ce mutum 10 aka sace amma sai kwatsam aka ga daruruwan yara.

Afenifere ta ce akwai tarin tambayoyi wanda duk wanda ya duba zai ga lallai akwai lauje cikin nadi a game da faruwar abun tun daga farkonsa har karshensa wasan kwaikwayo ne kawai da aka shirya domin wasa da hankulan yan Nigeria a cimma wata manufa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button