in , ,

Pantami ya umurci MTN,GLO,9M, Airtel su daina cazar kudi idan an duba NIN

Gwamnatin tarayya a karkashin ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki ta dakatar da kamfanonin sadarwa daga cazar Naira N20 -Ashirin da suke yi idan an danna lambobin ganin lambar dan kasa ta NIN.

Sheikh Ali Isah Pantami ya harmata masu wannan caji da suke yi sannan ya basu umurni kada su sake cazar ko sisi.

Saboda haka daga yanzu jama’a kuna iya duba ko layin wayoyin ku nada shaidar NIN kowane kamfanin sadarwa kuke amfani dashi ku danna *346# ku duba, DUBAWA DAGA YANZU KYAUTA NE!

Kalli hotunan daliban makarantar Kankara 340 da aka kubutar daga wajen Boko Haram

Irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi don magance mastalar tsaro