Labarai

Garba Shehu ya nemi afuwa kan cewa dalibai 10 aka sace a Kankara

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya nemi afuwa bisa bayanin da ya bayar a baya cewa dalibai 10 ne kawai aka sace a makarantar sakandaren Kankara ta jihar Katsina.

Manuniya ta ruwaito a wani sakon ban hakuri da Mista Garba ya fitar a yau Juma’a yana mai cewa “Ina neman afuwa kan kuskuren bayanai da na gabatar cewa dalibai 10 ne aka sace a makarantar kimiya ta Kankara.

“Wani ne wanda ya kamata ace ya sani ya bayar da bayanan kan adadin daliban wanda kuma yanzu ya ci karo da wadanda aka gani”

Jama’a da dama dai sun yi ta Allah-wadai bisa yadda mai magana da yawun shugaba Buharin ya fita kiri-kiri yana karyata Gwamnatin jihar Katsina wacce a lokacin tace akalla dalibai 333 ne amma Garba ya ce dalibai 10 ne kacal.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button