Labarai

PLATEAU: Gwamna Lalong ya kamu da korona ya mikawa mataimakinsa mulki

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya mika ragamar gudanar da mulkin jihar ga mataimakinsa Sonny Tyoden a yayinda shi kuma aka killace shi bayan sakamakon ya kamu da cutar koronaor

A wata sanarwa da Gwamnatin jihar ta fitar Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su cigaba da kiyaye kansu da daukar dukkan matakan da hukumar lafiya ta bayar na kare kai daga kamuwa da cutar korona

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ne kadai ya kamu da cutar koronar a cikin duka iyalansa da akayiwa gwajin cutar

“A wanke hannu a sanya takunkumin fuska sannan a kiyaye shiga cinkoson jama’a” inji Gwamnan

Lalong ya shiga jerin Gwamnonin da suka kamu da cutar korona, da suka hada da Gwamna Nasir El-Rufai jihar Kaduna, Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi; Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu; Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, Gwamnan Niger, da dai sauransu, kuma duk sun warke

A yayinda Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu, shima yake kan jinyar koronar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button