Labarai

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta kori Kwankwaso

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano bangaren tsohon ministan harkokin kasashen waje Aminu Wali, sun sanar da korar tsohon Gwamnan Kano jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga Jam’iyyar

Ana dai ta rikici a Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano tsakanin madugun Kwankwasiyyar da Aminu wali kan shugabancin PDP a Kano

Jami’iyyar PDP bangaren Wali ta zargi Kwankwaso da yin zagon kasa ga PDP kana kuma ta zarge shi da take dokokin Jam’iyyar

Manuniya ta ruwaito PDP ta kuma zabi sabbin shuwagabanni da zasu ja ragamar Jami’iyyar a jihar, to sai dai a daya bangaren kuma Kotu ta haramta Jam’iyyar PDP bangaren Aminu Wali a inda kotun ta ce PDP bangaren Kwankwaso ne halastacciyar Jam’iyya a Kanon.

A yanzu dai Mista Wali ya daukaka kara a inda ya kalubalanci wannan hukunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button