Labarai

DA DUMI-DUMI: Boko Haram ta saki bidiyon daliban makarantar Kankara

Kungiyar Boko Haram ta saki wani sabon faifan bidiyo mai tsawon mintuna 6 da dakika 30 na daliban makarantar kwana ta GSS Kankara wadanda mayakan suka sace a makon jiya.

Manuniya ta ruwaito a cikin bidiyon an ga Gomman daliban da kungiyar ta sace budi-budi da kura da daskararren jini a jikin rigar daya yaron da yayi magana a madadin sauran daliban, inda cikin yanayi na tashin hankali da tsoro ya roki Gwamnantin tarayya kada ta yi amfani da karfin soja wajen kokarin kubutar dasu daga hannun mayakan

Yaron wanda yayi magana cikin harshen Hausa da Turanci ya roki Gwamnati ta mika wuya ta bi duka sharuddan da mayakan suka gindaya domin sako su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button