Addini da RayuwaLabarai

Boko Haram sun saki daliban makarantar Kankara 340 da suka sace

Mayakan Boko Haram sun sako daliban makarantar da suka sace a makarantar Kankara dake jihar Katsina su 340

Manuniya ta ruwaito Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da labarin sakin daliban inda yanzu haka ake tafe dasu daga dajin jihar Zamfara zuwa Katsina a karkashin rakiyar jami’an tsaro.

Ana sa ran Gwamnan jihar Katsina Masari ne zai karbi yaran a daren yau a yayinda washe garin gobe Juma’a yaran zasu gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yanzu haka shima yake a cen garin Daura na jihar Katsina

Yaran budi-budi a cikin bidiyon

A dazu ne dai Boko Haram ta saki wani bidiyo mai tada hankali inda aka ga yaran suna rokon Gwamnati ta ceto su. Yaran sun roki Gwamnati ta bi hanyar lalama wajen ceto kada ta sa karfin soja

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button