Labarai

Wallahi sai na rushe duk wurin da na kama an bude –El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna ya sha alwashin rushe duk wuraren da Gwamnati ta hana a bude amma aka gano sun taka doka sun bude.

Gwamnan ya lissafo wuraren da aka umurci daga gobe Alhamis a rufe su baki daya, su ne, Gidajen rawa da kade-kade, kulub-kulub, wuraren shirya tarurruka wato event center’s, mashaya wato Bar, da kuma shirya manyan taruka duk an hana.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya kuma ce an rufe duka makarantu a fadin jihar Kaduna, daga kan na Boko har zuwa makarantun allo da na islamiyyu da na koyon sana’a har sai anga yadda hali yayi.

Elrufai ya kuma ce daga gobe sanya takunkumin fuska ga kowane dan mutum a jihar Kaduna ya zama wajibi duk inda mutum zashi ya sanya takunkumin sa, ya ce akwai hukumomi da zasu dauki mataki kan wadanda suka karya doka.

“A wancen karon mun samu rahoton wasu sun taka doka sun bude gidajen shakatawa, to wannan karon da kaina zan bi dare in duba, kuma duk inda na kama an bude toh Wallahi! Wallahi! Wallahi!! Washe gari sai na sa an rushe shi” -inji El-rufai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button