Album/EPLabaraiWasanni

El-Rufai ya rufe gidajen shakatawa da duka wuraren tara cinkoson jama’a a fadin jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanar da rufe wajajen shakatawa, kulub-kulub, da wajajen motsa jiki Gym, da kuma duk wajajen dake tara cinkoson mutane a fadin jihar.

Kazalika Gwamnan ya ce daga yanzu mutane ba zasu rika zama a gidajen abinci na Otel-otel da gidajen saida abinci (restaurant) ba kawai za a sayi abinci a tafi dashi ne.

Gwamnan har ila yau ya ce zasu cigaba da tabbatar da wajajen bauta, masallatai da coci-coci sun bi tsarin da aka sanya masu na cire tabarmun cikinsu ko carpet, sannan a rika bayar da tazara a lokutan ibada. Harwayau ya ce ya zama wajibi mutane su rika sanya takunkumin fuska kuma za a rika cin tarar duk wadanda suka taka doka.

Gwamnan ya kuma ce kasuwanni ma zasu bi duka tsare-tsaren kariya da aka gindaya masu.

Tu da farko dai Gwamnan ya ce sakamakon Gwajin da akayi masa na ranar Lahadi ya nuna bashi da korona. Idan dai ba a manta ba Gwamnan ya killace kansa bayan da aka samu iyalinsa da wasu makusantansa sun kamu da cutar korona.

Gwamnan ya kuma ce sai da sukayi wa duka wadanda suka halarci gasar tsere da akayi a kwanakin baya a jihar gwajin korona kafin yi da bayan yin tseren

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button