in ,

El-rufai ya haramta bin ‘one way’ a hanyar Kaduna- Abuja

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramtawa masu ababen hawa bin ‘one way’ a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A wata sanarwa da Gwamnatin ta fitar ta hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan a yau Laraba ya ce an baiwa jami’an tsaro dama su kama su hukunta duk mai ababen hawan da ya karya dokar

Sanarwar ta ce bin titi daya ko ‘one way ‘ da masu ababen hawa ke yi yana jawo hadarruka sannan yana baiwa yan bindiga damar kai hare-hare cikin sauki

DA DUMI-DUMI: Buhari ya bayar da umurnin a bude boda

El-Rufai ya rufe gidajen shakatawa da duka wuraren tara cinkoson jama’a a fadin jihar Kaduna