Labarai

EndSars: Zamu kashe Naira Biliyan 1 wajen gyara NPA -inji Hadiza Bala

Shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Nigeria NPA, Hadiza Bala Usman ta ce hukumar NPA tayi asarar fiye da Naira Biliyan 1 a rikicin zanga-zangar End Sars da ya auku a watan Octoba da ya gabata.

Hadiza wacce ke bayani a gaban majalisar dokoki ta tarayya ta ce za a kashe akalla Naira miliyan N807 domin gyara inda aka kona a lokacin rikicin.

Kana kuma akwai makudan kudade da za a kashe wajen sayo motoci 27 na hukumar wanda aka kona wasu kana aka sace wasu a rikicin zanga-zangar

Shugabar NPA din ta kuma ce an sace kayan aiki da na’urori, an sace kwamfutoci 317 da injinan yin Photocopy da dai sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button