in ,

DA DUMI-DUMI: Matsalar tsaro: Bala Lau ya umurci malamai su fara ruwan Alkunuti

Shugaban kungiyar Izala (JIBWIS) na kasa Sheikh Bala Lau ya ce komawa ga Allah da yawan istigfari ne kadai hanyar samun saukin kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan kasar nan musamman shiiyar Arewa maso Gabas da Arewa maso yamma.

Manuniya ta ruwaito Babban Malamin ya umurci Malamai su fara alkunuti domin neman taimakon Allah, “don haka, muna umurtar limamai na dukkan masallatan kungiyar JIBWIS su shiga jagorantar addu’o’in alkunut domin neman taimakon Allah, sannan mu rike gaskiya da amana za su karfafa karbar addu’o’in jama’a.” Inji Lau

“Kazalika mun bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da jami’an tsaro su yi tsayin daka kan kare rayuka, mutunci da dukiyoyin ‘yan Najeriya.”

Shugaban Jibwis na kasa Sheikh Bala Lau

“Muna jaddada ta’aziyya ga wadanda ‘yan Boko Haram  su ka hallaka a arewa maso gabar da buga misali da wadanda a ka yanka a Zabarmari, kazalika muna jajantawa iyayen ‘yan makarantar sakadandaren Kankara a Katsina da ‘yan bindiga su ka sace ‘ya’yan su, muna masu addu’ar samun kubutar yaran cikin salama.” Inji Shehin Malamin

Buhari yaki leka makarantar da aka sace dalibai amma ya ziyarci gonar shanunsa a Katsina

EndSars: Zamu kashe Naira Biliyan 1 wajen gyara NPA -inji Hadiza Bala