Shugaban kasa Manjo-Janaral Muhammadu Buhari ya ziyarci gonarsa a inda ya yi rangadi wajen shanun sa a jihar Katsina
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacinda aka sace daruruwan dalibai a makarantar Kankara dake jihar Katsina
Ganin bidiyon Buhari ya ziyarci shanun sa ya jawo cece-kuce a Nigeria musamman ganin yadda shugaban yaki ziyartar makarantar da aka sace daliban balle ma jajantawa iyayen yaran.


Mista Buhari dai ya isa garin Katsina tun makon jiya domin yin hutun karshen shekara a mahaifar tashi. Sai dai kwana daya da zuwan sa jihar ne sai yan bindiga suka sace dalibai akalla 600 kodayake dai zuwa yanzu wasu daga cikin daliban sun kubuce daga masu garkuwan sun koma gida.



