Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umurnin rufe duka manya da kananan makarantu na Gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar a matsayin wani mataki na dakile komowar cutar korona wacce adadin ta ke kara yawa a yan kwanakin nan a jihar da ma kasa baki daya.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta fitar a yau Litinin ta ce kowace makaranta a jihar ta tabbatar ta rufe daga ranar Laraba 16 ga watan Disamba 2020
Sanarwar ta ce dokar ta shafi duka makarantu har da jami’o’i da manyan makarantu a fadin jihar
