Labarai

An rufe hedikwatar sojin Nigeria bayan manyan sojoji 26 sun kamu da korona

Rundunar Sojin Nigerian ta ce kawo yanzu sakamakon gwaji ya nuna akalla sojoji 26 daga cikin mahalarta taron ta sun harbu da cutar korona a yayin da ake jiran sakamakon gwajin sauran.

A makon jiya ne ana tsaka da gudanar da taron shekara-shekara na shugaban sojin Nigeria kwatsam sai wani babban soja Manjo Janaral J.O. Irefin, ya fara zazzabi inda zuwa dare jiki ya tsananta cen kuma ya mutu a asibitin soji da aka kaishi.

Daga bisani Gwaji ya tabbatar da cewa korona ce ta kashe shi wanda hakan yasa dole aka tsaida taron inda aka umurci duka mahalarta taron su killace kansu

Sai dai zuwa yanzu anyi wa sojoji 417 gwaji inda sakamakon dake fitowa ya nuna 26 sun harbu,

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce tuni an kulle hedikwatar sojin sannan an yi ma ginin feshin rigakafin cutar, kana kuma duka sojojin na cigaba da killace kansu har zuwa a kammala gwaji da fitar da sakamakon gwajin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button