Sarkin Gona na jihar Gombe mai martaba Alhaji Umar Abdulkadir Abdulsalam (MNI) mai daraja ta daya, ya nada babban Dan jarida a jihar Gombe Abdulkadir Aliyu Shehu a matsayin Sarkin Bai Gona,

Abdulkadir Aliyu Shehu sanannen dan jarida ne wanda ke kula da sashin shirye-shirye na gidan Rediyon Progress dake Gombe.
Abdulkadir wanda aka fi saninsa da Prince dai tsatson Dabo ne a masarautar Kano.
Prince har wayau shi ke gabatar da shirin Tumbin Giwa a tashar Progress FM.