in , , ,

Matasa 11 sun mutu a hanyar zuwa jarabawar shiga aikin soja a Kano

Mutum 11 sun mutu a wani hadarin mota da ya rutsa dasu a hanyar Kano zuwa Jigawa, matasan na tafe ne zasu je Kano daga kauyen Gagarawa domin jarabawar shiga aikin Sojan sama

Manuniya ta ruwaito kakakin yan sanda na jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya ce hadarin ya auku ne a lokacinda motar da matasan ke ciki wata Golf 3 wagon, ta afka karkashin wata babbar motar DAF dake tsaye a titin ta lalace

Wadanda hadarin ya rutsa dasu sun hada da, Auwalu Mohammed (Dreban motar tasu); Mutari Sule; Ibrahim Sani; Katimu Muhammad; Dauda Salisu; Musbahu Yakubu, Rabiu Muhammad-Ado; Salim Muhammad-sani; Akibu Ubali-sale; da Murtala Salisu, da kuma wani cikinsu da ya rasu a asibiti

Manuniya ta ruwaito Kakakin yansandan na cewa tuni sun kama dreban babbar motar Aminu Hassan, domin.

Gawar matasan gabanin ayi masu janaiza

Matasan sun bar gida tun wajajen karfe 5 na asubahin ranar Asabar da nufin su isa Kano da wuri domin su samu su yi jarabawar shiga sojan

Hoton wasu daga cikin margayin yaran

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya kamu da cutar korona

Kalli gasar da Aisha-Ummi El-Rufai ta shirya kan yaki da fyade da cin zarafin jinsi