Labarai

KATSINA: Mun san inda aka boye daliban da aka sace — inji Ministan tsaro

Ministan tsaro na Nigeria, Manjo Janaral Bashir Magashi (murabus), ya ce kawo yanzu suna da labarin inda daliban makarantar GGSS, Kankara da aka sace suke, kuma yana mai tabbacin zasu kubutar dasu nan bada jimawa ba.

Mista Magashi, ya ce a yanzu addu’a kawai suke nema domin kammala ceto daliban ba tare da wani kalubale ba.

Ministan ya fadi haka ne a lokacinda ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya zuwa jihar Katsina a yau Lahadi.

Manuniya ta ruwaito tawagar da ta ziyarci jihar sun hada da Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Maj.-Gen. Babagana Monguno da shugaban hafsoshin tsaro, Gen. Abayomi Olonisakin da shugaban sojin sama Air Marshall Sadique Abubakar, da shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas

Sauran sun hada da Sufeta-Janar na yan sandan Nigeria Mohammed Abubakar, da Darakta Janar na yan sandan farin kaya Yusuf Magaji-Bichi da Darakta Janar na cibiyar tattara bayanan sirri na kasa Ahmed Rufai.

Yan bindiga dai sun kai farmaki makarantar kwana ta maza dake Kankara a jihar Katsina inda suka sace dalibai da dama da ake zargin sun zarta 300.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button